Your shopping cart is empty!
Amarzadan a Birnin Aljannu
By Bashir Othman Tofa
Wannan littafi, shi ma, kamar na 'Gajerun Labarai' ne, labaran da ke ciki, dukkansu qagaggu ne kuma almara, an qaga su ne domin nishaxantar da mai karatu. A cikin labaran, marubucin ya yi amfani da fasaha da qwarewa wajen isar da saqwanni daban-daban domin amfanin al'umma. Haka kuma, ba a rubuta wannan littafi don cin fuska ga wani ba. Waxanda za su fi more wa wannan littafi su ne waxanda suke iya ayyana abubuwan da aka misalta a cikinsa, sannan su xauke shi tamkar waqi'i (gaskiya), duk kuwa da cewa sun san ba gaskiya ba ne.